1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DUBBAN BAKIN HAURE NA KWARARA ZUWA TURAI TA SPAIN DA MOROKKO DAGA AFRIKA.

August 18, 2004

Ana cigaba da fuskantar matsalar kwararan bakin haure zuwa kasashen turai,musamman daga yankunan Sahara da Afrika.

Bakin Haure a gabon tekun Spain.
Bakin Haure a gabon tekun Spain.Hoto: AP

Daga arewacin kasar Moroko ,tafiya kalilan ce ta teku,zaa fada yankin turai ta Spain,inda bakin haure daga kasashen Afrika ke amfanin da hanyar wajen shiga kasashen turai.

A makon daya gabata kusan bakin haure sama da 500,suka nemi kutsawa wasu karafe dake raba arewacin moroko da Spain.Gwamnatin Rabat dai ta amince da wannan yunkuri sai dai tace mutanen basu wuce 60 ba.kalilan daga cikinsu dai rahotanni sun tabbatar dacewa sun samu nasaran kutsawa cikin Spain ta Melilla ,ayayinda sauran kuma aka maidasu Moroko.

Hukumomin Melillan dai sun bayyana cewa a yanzu haka akwai kimanin mutane 700 daga kasashen Mali,Cameroun,Niger,Senegal da Nigeria,dake wani sansani akan duwatsu dake kallon wannan birniAkasarinsu kuwa sun kasance kann wadannan duwatsu ne na tsawon shekaru masu yawan gaske,kuma sun sha kokarin keta kann iyakar Spain din ba tare da cimma nasara ba.

Magabatan Melilla da makwabciyarta Ceuta dai ,na fuskantar matsalolin kwararan bakin haure dake kokarin shiga kasashen turai,ta kwale kwale ko kuma a manyan motoci ta kungurmin jeji.

A yanzu haka dai rahotanni sun tabbatar dacewa akwai yan Afrika daga kasashe daban daban kimanin dubu 5 dake zama acikin jejinan Tangiers dake kasar Morokko,kusa da gabar tekun Melilla da Ceuta dake kasar Spain,suna jiran ranar da kakarsu zata yanke saka su fada turai.

Shugaban kungiyar dake lura da iyalan bakin haure Khalid Jemmah,ya koka dangane da halin kuncin rayuwa da waddanan mutane ke rayuwa ciki a tsakanin itatuwa.Yace duk da irin wahala da barazanar jamian tsaro,a kullum zaka samu karin sabbin bakiun haure dake jiran ranar cimma burinsu na kutsawa kasashen turai ta wannan hanya.

Bugu da kari masu fataucin mutane,wadanda mafi yawan su na daga Afrika da yankunan sahara na amfani da wannan hanya wajen safaran mutane.Ayanzu haka dai masu jiragen ruwa na karban akalla dalan Amurka 1200,kwatankwacin euro 1000 kenan,saboda hadari dake tattare da aikin da sukeyi na tsallakar da bakin hauren.

Ta kudanci kuwa dubbannin mutane ne kebi takan tsibirin Canary Spain,wanda nan ma wata hanya ce ta shiga kasashen turai.An kiyasta cewa tsakanin watannin janairu zuwa yuli kadai ,kimanin mutane 3,300 a dakatar daga bin wannan tsibirin ba bisa kaida ba.Akasarin bakin hauren dai sun gwammace bin tsibirin na canary mai tazarar km 160,wanda ke gabon kogin moroko.

Koma dai wane hanya suke bi,dubban bakin haure ne ke ketawa zuwa kasashen turai akowace shekara,sai dai a shekarar data gabata,kimanin mutane 500 suka rasa rayukansu,a kokarinsu na shiga Spain.A dangane da karuwan wannan yanayi ne a farkon wannan shekara moroko da spain suka amince da kaddamar da sintiri na hadin gwiwa kann iyakokin nasu.A halin da ake ciki yanzu haka dai akwai jirage kirar saukan ungulu na yansandan kasasahen biyu dake sintiri ,a gaban tekun banda jiragen ruwa na yansanda dake yawo tsakanin tsibirin Canary da yammacin sahara.

Zainab Mohammed.