Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya
May 25, 2024Sama da masu neman mafaka mutum dubu 10 suka shiga kasar Burtaniya a wannan shekarar cikin kananan jiragen ruwa, wani abu da ke nuna jan aiki da ke iya shafar Firaminista Rishi Sunak a zaben watan Juli.
A shekarar da ta gabata ne aka lura cewa adadin masu shiga kasar ta hanyar tafiyar kasada sun ragu, sai kuma ga shi sabbin alkaluma da aka wallafa a shafin gwamnti na nuna mutum dubu 10 da 170 sun kutsa kasar daga farkon watan Janairu zuwa yau 25 ga watan Mayu.
A baran dai bayanai sun nuna cewa mutum dubu bakwai da 395 baki suka shiga Burtaniyar a daidai wannan lokaci.
Firaminista Rishi Sunak, wanda ya sanar da ranar zabe a Larabar da ta gabata, ya bayyana cewa duk wani mai neman mafakar da ya shigo kasar ba bisa ka'ida ba, ya sani cewa za a aika da shi kasar Ruwanda kafin lokacin zaben.