1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Dubban magoya bayan gwamnatin Iran sun yi dafifin mubaya'a

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 12, 2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ta tuntube shi don tattauna yadda za a magance boren, bayan mutuwar mutane 544.

Cincirundon masu zanga-zangar adawa da rayuwa a Iran
Cincirundon masu zanga-zangar adawa da rayuwa a IranHoto: UGC

Dubban jama'a magoya bayan gwamnatin Iran, sun yi dafifi a wannan rana ta Litinin, a dandalin juyin-juya-hali na Enghelab da ke tsakiyar Tehran babban birnin kasar, domin zanga-zangar lumana da ke nuna amannarsu da mahukuntan kasar, tare da alhinin jami'an tsaron da suka rasa rayukansu, a yayin boren adawa da tsadar rayuwa.

Wasu hotuna da gidan talabijin din kasar ya haska, sun nuna yadda dubban mutanen rike da tutucin Iran, ke addu'o'i ga mamatan, haka zalika ana gudanar da wasu tarukan makamantan wannan a sauran biranen kasar, bayan kiran da shugaba Masoud Pezeshkian ya yi, na yin hakan.

Karin bayani:Iran: Shugaban kasa ya nemi zama da masu zanga zanga

Tuni aka jiyo shugaban Amurka Donald Trump na cewa Iran ta tuntube shi, don tattauna hanyoyin magance wannan tarzoma, bayan mutuwar kimanin mutane 544, a yayin wannan zanga-zanga da ta rikide zuwa neman sauyin gwamnati.