1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dubban matasa ke mutuwa a Tsibirin Canary-UNHCR

September 28, 2024

Akalla mutane tara sun mutu bayan da wani jirgin kwale-kwale ya kife da 'yan gudun hijra a tsibirin Canary a yunkurin matasan na shiga nahiyar Turai daga kasashen Afirka.

Wasu matasa da ke kokarin tsallakawa Turai ta tsibirin El Hierro
Wasu matasa da ke kokarin tsallakawa Turai ta tsibirin El HierroHoto: Europa Press/AP Photo/picture alliance

Masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane 27 daga cikin sama da 80 da ke makare a cikin kwale-kwalen, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutanen kimanin 48 a gabar tsibirin El Hierro.

Karin bayani: Spain ta ceto 'yan ci-rani 516 daga Afirka a tsibirin Canary

Hukumar kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce sama da mutum 30,000 suka isa tsibirin na Canary a iya wannan shekarar ta 2024. Hukumar kididdigar 'yan gudun hijra ta Spain ta ce mutane sama da 4,800 sun nutse a ruwa daga watan Janairu zuwa Mayu.