Dubban mutane sun warke daga coronavirus
April 6, 2020Talla
Kamar dai yadda bayanan da Jami'ar John Hopkins da ke bin diddigin yaduwar cutar da ke Amirka suka nunar, ya zuwa wayewar garin Litinin, akwai mutum fiye da miliyan daya da dubu 200 da cutar ta kama a fadin duniya.
Jami'ar ta kuma ce kimanin mutum dubu 70 ne kuma cutar ta kashe a sassa daban-daban na duniyar, musamman ma a kasashen da annobar ta fi tsanani a cikinsu.
Kasashen da lamarin ya fi munanan a cikinsu dai su ne Amirka da Spain da Italiya, sai Jamus da Faransa sannan sai kasar China.
Haka ma akwai kasashen irin su Iran da Birtaniya da Turkiyya sai kuma Switzerland.