Dubban sojojin Rasha sun mutu a Ukraine
May 2, 2023Talla
Akalla sojojin gwamnatin Rasha da na haya su dubu 20 suka mutu a yankin Bachmut da ke a gabashin Ukraine, a cikin watanni biyar da suka gabata, a cewar wasu alkaluma da Amurka ta fitar.
Haka ma a cewar alkaluman akwai karin wasu mayaka dubu 80 da suka jikkata a wannan tsuki.
Hukumar leken asiri ta Amurka ta ce rabin asarar sojojin dai ya shafi wadanda ke mallakin kamfanin nan na Wagner, kamar yadda shugaban majalisar tsaron Amirka John Kirby ya nunar.
A share guda kuwa, ministan tsaron kasar Ukraine Olexiy Resnikov, ya ce shirye-shirye sun yi nisa game da sake kwato yankunan da ke hannun Rasha a yakin da kasashen biyu ke gwabzawa.