1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan adawa na kalubalantar Alassane Ouattara

Abdourahamane Hassane
August 9, 2025

Dubban 'yan adawa sun gudanar da gangamin lumana a birnin Abidjan na Cote d'Ivoire, domin nuna adawa da yunkurin shugaba Alassane Ouattara mai barin gado, na neman yin wa'adi na hudu,

Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

'Yan adawar na  kuma neman a maido da wasu ' yan adawa da dama daga cikin jerin sunayen 'yan takara na zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 25 ga watan Oktoba.

Jam'iyyar Dimokuradiyya ta Cote d'Ivoire (PDCI) da Jam'iyyar  jamaar Afirka   ta (PPA-CI) su dukkaninsu an cire sunayensu daga zaben. Wato , Tidjane Thiam da Laurent Gbagbo.

An ciresu daga takarar shugaban kasa ta hanyar yanke hukunci na kotu, na farko game da rashin takardar shaidar zama da kasa, yayin da Laurent  gbagbo kotun ta ce,yana a karkashin hukuncin shari'a.