1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban 'yan Boko Haram sun mika wuya a Najeriya

December 13, 2024

Hukumomi a Najeriya, sun ce kimanin mayakan kungiyar Boko Haram dubu 130 ne suka ajiye makamansu a cikin watanni biyar da suka gabata a kasar.

Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa da wasu manyan jami'ai
Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa da wasu jami'aiHoto: KOLA SULAIMON/AFP

Hafsan hafososhin kasar Najeriya, Janar Christopher Musa shi ne ya fadi hakan a lokacin wani taro kan al'amuran tsaro da ya halarta a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Alhamis.

Janar Christopher Musa ya ce a tsakanin ranar 10 ga wata watan Yuli zuwa 9 ga watan nan na Disamba, mayakan Boko Haram dubu 30 da 429 da mata dubu 36 da 774 da kuma yara dubu 62 da 265 su ne suka mika wuya.

Taro ne dai da aka yi a kasar ta Qatar da ya yi nazari kan halin tsaro musamman na kasashen Afirka.

Rundunar sojin Najeriya dai ta ce an yi nasarar samun mika wuyan ne, bayan matakan tattaunawa da sake tunani da aka dauka domin 'yan bindiagr da suka tuba, abin kuma da ya ce ana ganin fa'idarsa.