1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubunnan yan gudun hijira daga Siriya na kwarara Turkiyya

June 15, 2011

Hare-haren kan mai uwa da wabi da sojojin Siriya ke yi kan al´umar arewacin kasar ya cilastawa dubunnai shiga gudun hijira a Turkiyya da Lebanan

Hoto: AP

Dubunnan al´umomin dake zaune  a yankin arewacin Siriya na cigaba da tsallakawa zuwa kasashen Turkiya da Lebanan domin kauracewa kisan gillar sojojin shugaba Basahr Al-Assad.

A waje daya, magoya bayan shugaban sun shirya wani kasaittacen jerin gwano a birnin Damaskus domin shaidawa duniya cewar Assad shima ya na da masoya.

A yayin da ya ke tsokaci game da kwawarar mutanen Siriya zuwa Turkiyya ministan harakokin wajen Turkiyya, Ahmat Davutoglu cewa yayi Turkiya ba za ta rufe iyakokinta ba:

"Za mu cigaba da karbar yan gudun hijira daga Siriya, amma mu na kira ga gwamnatin Siriya ta tausaya ta daina kai hari ga jama´arta."

Daga cikin yan dugun hijirar har da sojojin da suka burjinewa gwamnati, wanda kuma suka ce a na cilasta masu ne aikata hare-hare ga fara hula

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal