1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na dumama fiye da yadda ake tsammani

Abdullahi Tanko Bala
September 23, 2019

Yayin da shugabannin kasashen duniya suka hallara domin fara babban taro kan sauyin yanayi a birnin New York masana kimiyya sun yi gargadin cewa sauyin yanayi na karuwa fiye da yadda ake tsammani.

USA Greta Thunberg in NewYork
Greta Thunberg deltar på FN klimat toppmöte för unga i...
Hoto: picture-alliance/TT NYHETSBYRÅN/P. Lundahl

A wani rahoto da ta fitar hukumar kula da yana yi ta duniya ta nuna cewa a 'yan shekaru da suka wuce yanayin zafi ya karu yayin da koguna da koramus uka cika makil sannan gurbatar hayakin masana'antu ya karu matuka.
   
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci rage hayakin Carbon nan da shekara ta 2050 domin tsaftace muhalli daga gurbatacciyar iskar.

A waje guda kuma kasashen Afirka za su gabatar da kiran ayyana dokar ta baci kan muhallin domin taimaka musu kare illomin gurbatar muhalli a nahiyar.