1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Chadi ta bi sahun yaki da cin hanci a duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 9, 2025

Chadi ta bi sahun kasashen duniya wajen wajen raya ranar yaki da cin hanci da karbar rashawa. cin hanci da rashawa na haddasa illa musamman ga fannin tsarin shari'a a Chadi.

Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Galibin 'yan Chadi na daukar fannin shari'a a matsayin daya daga cikin cibiyoyi mafi cin hanci da rashawa a kasar. Ko da shari'o'in da suka gabata a baya-bayannan, an gurfanar da manyan jami'an soji biyar a shari'ar da ta shafi yunkurin ba da na goro ga wani alkali mai bincike. Sannan ma'aikatar shari'a ta dakatar da alkalai shida sakamakon zarginsu da cin hanci da rashawa a wata shari'a da kuma rashin halartar wuraren aikinsu akai-akai.

Babban magatakarda a babbar kotun N'Djamena babban birnin Chadi Doudjimsengar Tatolnan, ya ce wannan badakalar karbar cin hanci a shari'o'in na kara bata sunan tsarin shari'ar kasar a idanun jama'a.

Karin Bayani: Kokarin yaki da cin hanci da rashawa a yammacin Afirka

Babbar kotun tarayya a N'Djamena kasar ChadiHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP/Getty Images

"Akwai rashin yarda ko amincewa da tsarin shari'a, saboda haka ne 'yan kasar Chadi suka fi son sasanta al'amuransu a ofisoshin 'yan sanda da rundunonin Jandarmomi, domin tsarin shari'a ba mafaka ba ce ta aminci. Ya zama mafaka ga 'yan daba da masu zamba. Cin hanci da rashawa da muke magana a kai a tsarin shari'a, abu ne na zahiri. Ta ya ya alkalin da ke bincike zai tattauna kan shari'a da nufin zambatar mutane da karbar kudi? Wannan babu adalci a ciki. Amma a gaskiya, ba alkalai ne kawai ke aikata cin hanci da rashawa ba. Akwai kuma lauyoyi da ke taka muhimmiyar rawa a cin hanci da rashawa, da kuma jamai'an gwamnati masu ba da beli da magatakarda na kotu. Duk tsarin shari'a na bukatar gyara."

Amma sakamakon girman matsalar cin hanci da rashawa a tsarin shari'ar kasar Chadi, wasu fitattun mutane, ciki har da ministan Shari'a na yanzu Youssouf Tom, sun kafa wani tsarin yakar wannan ja'iba mai suna cibiyar yaki da cin hanci da rashawa.

Karin Bayani: Yaki da cin hanci da rashawa a duniya

Shugaban Chadi Mahamat Idriss Déby Itno Hoto: Abd Rabbo Ammar/ABACAPRESS/IMAGO

Hamane Bouba Wabang, da ke jagorantar wannan cibiya, ya bayyana wasu daga cikin matakan da yake shirin dauka don dawo da mutuncin tsarin shari'a tare da raba ta da matsalar cin hanci da rashawa.

"Mu, jakadun yaki da cin hanci da rashawa, muna ba da shawarar daukar wadannan matakai a nan gaba. Wayar da kan jama'ar kasar Chadi game da illar annobar cin hanci da rashawa a fannin tsarin shari'a da sakamakonta, da isar da bayanai da koke-koken 'yan kasa ga hukumomin da suka dace da ke kula da fannin shari'a, da kuma daukar matakin a rubuce don bayar da rahoton ayyukan cin hanci da rashawa a fannin shari'a ga hukumomin da suka dace."

Wasu masu ruwa da tsaki na kasar Chadi sun yi Allah wadai da tasirin siyasa wanda ke hana sashen shari'a rawar gaban hantsi, duk da kasancewar dokoki da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani