Martanin duniya kan tsagaita bude wuta a Iran
April 8, 2026
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi maraba da tsagaita wuta na wucin gadi da aka cimma tsakanin Washington da Tehran bisa shiga tsakanin Pakistan. Guterres ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikicin da su mutunta dokokin kasa da kasa tare da bin sharuddan yarjejeniyar domin samun zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya.
Ita ma babbar jami'ar diflomasiyyar Tarayyar Turai Kaja Kallas, ta yaba da tsagaita bude wutar, tare da tabbatar da cewa EU na a shirye domin ba da gudummowa wajen komawa kan teburin tattaunawa.
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce yanzu ya kamata a mayar da hankali kan tattaunawar kawo karshen yaki na dindindin, yana mai jaddada cewa hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar diflomasiyya, yayin da Chaina ta ce za ta ci gaba da kokari don dawo da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
A nasa bangare shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Mahamoud Ali Youssouf, ya ce wannan tsagaita bude wuta wata muhimmiyar dama ce don rage wahalhalun al'umma, yana mai kira da a ci gaba da tattaunawa domin samar da zaman lafiya mai dorewa.