1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sarki Charles na fama da cutar sankara

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 6, 2024

Firaminista Rishi Sunak na Birtaniya, ya mika sakon jinjina ga Sarki Charles na III da likitoci suka gano yana dauke da cutar sankara.

Sarkin Charles na III | Birtaniya | Rashin Lafiya
Sarkin Charles na IIIHoto: Victoria Jones/empics/picture alliance

Firaminista Rishi Sunak  ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa, ga sarkin mai shekaru 75 a duniya. Tuni shugabannin kasashe da dama na duniya, suka aike da irin wannan sakon ga sarkin bayan gano yana dauke da cutar ta sankara. Kimanin shekara guda da rabi ke nan dai, Sarki Charles na III na Birtaniya ya gaji mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth. Sanarwar rashin lafiyar tasa dai, ta jijjiga mutane a cikin kasar da har yanzu tsarin masarautar ke da tasiri matuka. Jaridun Birtaniya duk sun mayar da hankali kan cutar da ta kama sarkin, tare da fatan cewa zai samu sauki.