Coronavirus : Za a iya samun mutuwa a kasashe masu rauni
March 19, 2020
Talla
A wani taron manema labarai da ya kira ta bidiyo babban sakataran Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce idan har aka bari, kwayoyin cutar Coronavirus suka bazu kamar wutar daji zuwa cikin kasashe masu rauni miliyoyin mutane ne za su mutu. Ya ce duniya na fuskantar barazana ta Covid 19 ya zama wajibi mu ba da gudunmawa don ceton rayuka.