Duniya na cikin hadarin fuskantar karancin makamashi - IEA
March 23, 2026
Hukumar makamashi ta duniya IEA ta yi gargadin cewa yakin da ake ci gaba da gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya na iya haddasa gagarumar matsalar makamashi mafi nuni da ba a taba fuskanta ba a duniya.
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta sanar da kara yin damara domin ci gaba da gwabzawa har zuwa wasu makwanni a nan gaba, tare da kai sabbin hare-hare kan Teheran babban birnin Iran.
Shugaban Hukumar Fatih Birol, ya ce ''i zuwa wannan lokaci ana rasa gangar mai miliyan 11 a kowace rana sakamakon toshe mashigin Hormuz, lamarin da ya zarta matsalolin makamashi guda biyu da duniya ta yi fama da su a shekarun 1970.''
Shugaban hukumar ta IEA ya kara da cewa babu wata kasa da za ta iya tsira daga wannan matsala inda aka ci gaba da yaki, a don haka ya zama wajibi duniya ta yi taron dangi domin yi wa tubkar hanci.
Amurka ta dage takunkumi kan man Iran na wucin-gadi
A cewar hukumar bincike ta Kpler zirga-zirgar kayayyaki ta ragu da kashi 95% a mashigin Hormuz wanda kaso 20% na makashin da duniya ke amfani da shi ke wucewa ta cinkinsa.
Trump ya ba wa Iran wa'adin bude mashigin Hormuz ko ta dandana kudarta
Iran na ci gaba da yi wa kasashen yankin Gulf barin wuta
Ma’aikatar Tsaron Saudiyya ta sanar da cewa a safiyar nan ta Litinin an harba makamai masu linzami guda biyu zuwa Riyadh, a rana ta 24 da barkewar yakin yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da wasu kasashen yankin Gulf su ma suka ba da rahoton cewa Iran ta harba musu makamai.
Sai dai ma’aikatar tsaron ta Saudiyya ta ce an dakile guda daga cikin makaman, yayin da gudan ya fado a wani wuri da babu mutane.
Haka zalika ita ma ma’aikatar tsaron Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa a yanzu haka tana ci gaba da dakile barazanar makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka da Iran ta harba wa kasar.
A gefe duda kuma ma’aikatar cikin gida ta Bahrain ta gargadi 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu sannan kuma su zauna a guraren da aka tanada domin buya.
Iran dai na ci gaba da kai hare-hare ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka da muhimman ababen more rayuwa a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa da kuma wuraren hakar man fetur.