Yawan kudaden da ake kashewa wajen sayen kayan yaki ya karu
February 15, 2020Talla
Rahoton ya ce a cikin shekaru goma ba taba ganin irin haurawar ba ta yawan makamai a duniya. Kasashen Amirka da China na kan gaba a sahun kasashen da suka fi kashe kudade a harkokin soji wajen sayen makamai. Shugaban Kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a lokacin bikin bude taron ya ce a kwana a tashi duniya na yi nesa da irin alkawarin da aka dauka na samar da zaman lafiya sakamakon yake-yake da tashin hankali da duniyar ke fuskanta.