Duniya na jimamin harin ba zata da Hamas ta kai a Isra'ila
October 7, 2025
Hamas ta kai harin ba zata a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, mummunan harin ya kashe mutane fiye da dubu daya da 200 ciki har da fararen hula da garkuwa da wasu da dama.
Isra'ila na tunawa da harin 7 ga Oktoba
A jawabinsa a albarkacin wannan rana, Firaministan Spain Pedro Sánchez, ya yi Allah wadarai da harin ta'addanci kowane iri, tare da kira ga shugaban gwamnatin Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya kawo karshen yakin da kasarsa ke yi a Gaza,
Shi ma shugaban gwamnatin Jamus Fredrich Merz, yayin jawabinsa na tunawa da cikar shekaru biyu da harin 7 ga Oktoba, gargadi ya yi dangance da yadda ake samun masu kyamar Yahudawa a Jamus, tare da nuna jimamin yadda ranar ta kasance a shekaru biyu.
Trump ya bukaci a gaggauta samar da zaman lafiya a Gaza
Inda ya ce "Ranar 7 ga watan Oktoba ta shekarar 2023 ta bar raunuka masu radadi, ta kasance a cikin kudin tarihi ga Yahudawa a matsayin ranar bakin ciki da bacin rai. Shekaru biyu da suka wuce a wannan rana, kungiyar Hamas ta kai hari mai zafi kan Isra'ila. Fiye da ‘yan kasar 1,000 sun rasu ciki har da mata da yara da matasa da jami'an tsaro."