1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na martani kan tsagaita wuta a Zirin Gaza

Maawiyya Abubakar Sadiq M. Ahiwa
October 9, 2025

Yayin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin Isra'ila da Hamas, bayan shefe shekaru biyu na rikici, shugabannin kasashen duniya na ta martani da fatansu dangane yarjejeniyar da aka cimma.

Yadda wasu Falasdinawa a yankin Khan Younis ke murna bayan sanar da matakin farko na tsagaita wuta
Yadda wasu Falasdinawa a yankin Khan Younis ke murna bayan sanar da matakin farko na tsagaita wuta Hoto: Ramadan Abed/REUTERS

Wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya da suka yi tsokaci sun hada da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz inda ya ce kasarsa  na nazarin halin da ake ciki dangane da cimma wannan yarjeniya ta Gaza, amma akwai yakinin za a samu mafita a cikin wannan mako.

 ''Muna samun karfin guiwa dangane da ci gaban da ake samu a Isra'ila, a bayyana take an samu gagarumin ci gaba na cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas''                                           

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce; "Majalisar Dinkin Duniya za ta goyi bayan aiwatar da yarjejeniyar gaba daya. Kuma za ta kara yawan isar da kayan agajin jinkai mai dorewa da ka'ida, kuma za mu ci gaba da kokarin farfadowa da sake gina Gaza," 

Firaministan Canada Mark Carney, Ya ce ya ji dadin cewa nan ba da jimawa ba wadanda aka yi garkuwa da su za su sake haduwa da iyalansu.

"Bayan shekaru na wahala mai tsanani, zaman lafiya a karshe yana kama da abin da za a iya samu. Canada na kira ga dukkan bangarorin da su gaggauta aiwatar da dukkan sharudan da aka amince da su, da kuma yin aiki don samun adalci da zaman lafiya mai dorewa."

Deir al-Balah 2025 | Falasdinawa na murnar dakatar da yaki a gaban Asibitin Al-AqsaHoto: Abdel Kareem Hana/AP Photo

Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim a cikin wata sanarwa ya ce‚ ‘‘bayan watanni na wahala da barnar da ba za a iya jurewa ba, "ya bukaci dukkan bangarorin da su yi amfani da wannan damar don ci gaba, zuwa ga cikakken zaman lafiya mai dorewa.

Ita ma kasar China a ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajenta, Guo Jiakun, ya yi tsokaci yana mai cewa:

''China na fatan za a samun tsagaita wuta na dindindin a zirin Gaza, a farkon lokaci don rage radadin jin kai, da tashin hankali a yankin. China tana goyon bayan ka'idar 'Falatsinawa suna mulkin Falatsinu,' kuma tana inganta aiwatar da mafita ta kasashe biyu.

Kasar Japan a ta bakin babban sakataren gwamnati Yoshimasa Hayashi ya ce; "Japan na maraba da cewa an cimma yarjejeniya a 'mataki na farko' a tsakanin bangarorin da abin ya shafa. Wannan yarjejeniya muhimmin mataki ne, don rage tashe-tashen hankula da kuma cimma mafita ta kasashe biyu"

Firaministan Australia Anthony Albanese ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "hasken bege". Ya ce sanarwar ta kawo karshen shekaru tamanin na rikici da ta'addanci. Za mu iya karya wannan zagaen tashin hankali da gina wani abu mafi kyau.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani