1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na nazartar jawabin Shugaba Trump

Usman Shehu Usman
March 1, 2017

Kamar yadda aka yi hasashen batun 'yan gudun hijira da tsarin inshorar lafiya na gwamnatin baya, wato Obamacare na daga cikin abin da ya mamaye jawabin shugaban da har yanzu ake ganin bai sauya ba a akidunsa.

USA Donald Trump vor dem US-Kongress in Washington
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Lo Scalzo

A jawabin nasa na farko gaban majalisar dokoki, Shugaba Donald Trump ya yi kokarin wanke kansa daga zargi da ake yi masa na kyamar tsiraru a kasar, inda ya fara jawabin nasa da bayyana tunawa da gwagwarmayar bakaken fatar Amirka, kana ya ce akwai sauran tafiya wajen kammala aikin kwatar 'yancin kungiyoyin fafitika. Ya kuma yi tsokaci kan farmakin da aka kai a wuraren baki da kuma barazanar da aka fara yi wa Yahudawa, wadanda duk ake zargin Amirkawa zauna gari banza da ke goyon bayan Trump suka aikata. To sai dai duk da sassaucin da aka ji daga bakin Trump a jawabin na jiya, wasu na ganin ba wai ya na nufin shugaban na Amirka ya fara yin nadama ba. David Litt shi ne ke rubutawa tsohon shugaban Amirka Barack Obama jawabai da ya ke gabatarwa.

An dai dauki lokaci ana adawa da shirin Trump na fatali da shirin ObamacareHoto: picture-alliance/dpa

"Trump a wannan jawabin ya dan sassauta kalamansa. Amma fa shi ba zai canja ba. Idan mutum ya saurari jawaben nasa da kunnen basari zai fahimci duk kalaman da ya fada abu ne da tuni ya taba ambantonsu. tun a lokacin da ya ke takarar zabe. Kai a ganina babu wani sabon abu da ya fada. Kuma a ra'ayina babu wata fatan sauyin demokradiya, ko fata  na gari da hakan ya nunar."

Daga cikin jawaben nasa dai Trump bai fasa ikirarin da ya ke yi na cewa Amirka farko kafin komai ba, ma'ana ba ruwansa da wasu al'amuran da Amirka ke sa hannun kansu a kasashen waje, illa kawai a inganta karfin Amirka a duniya, batun da Jake Sullivan mai bai wa tsohon mataimakin shugaban kasar Amirka Joe Biden shawara kan tsaro ya bayyana cewa.

Kasashe da dama na adawa da tsarin sojan Amirka a kasashensuHoto: Getty Images/AFP/Jung Yeon-Je

"Indan mutum  ya kawar da tsarin diflomasiya da taimkon raya kasa, cikin manufofin huldar kasashen wajen Amirka, to abin da zai saura sai karfin soja kawai. Kuma idan mutum ya ce shi ya dogara kacokan bisa karfin soja, to duk wane sabani ko jayayya da aka yi, sai a fara yaki kawai. Ta hakan kuwa zai ci gaba da ruruta tashin hankali da yake-yake a duniya ne kawai."

Matsalar ta shugaban kasar Amirka za'a iya cewa kusan ta mamamye duniya ciki har da manyan kawayen Amirka, kuma hakan na nufin rigimar ta biyo bayan Trump ta fi karfin ta tsakanin 'yan democrat da republican kamar yadda Nico Lange jagoran gidauniyar Konrad-Adenauer ta Jamus a birnin Washington,ya bayyana.

"Rigimar da ke gaba a makonni ko watanni da ke tafe ta fi karfin adawa tsakanin jam'iyyun kasar, kamar yadda Trump ke kokarin cewa Democrat ce ke ingaza kiyayya kansa. Amma rigimar ta na nan tsakanin su 'yan republican tsakanin masu tsattsauran ra'ayi da masu sassauci."