Duniya na yaki da yi wa mata kaciya
February 6, 2018A gundumar Gaya cikin jihar Dosso mai makwabtaka da Jamhuriyar Benin wata mata ta bayyana yadda har yanzu ake yi wa mata kaciya a cikin kauyensu da ke tsakanin iyakar Nijar da Benin duk da cewa akwai masu adawa da hakan. Sai dai sannun a hankali za'a iya cewa an samu koma baya sosai a kan wannan dadadiyar al'ada. Wasu mata da ke cikin wadanda aka yi wa kaciya, wanda tuni aka yi musu aure a halin yanzu, sun danganta lamarin da mafi muni a cikin harkokin rayuwarsu, domin a cewarsu ba su da wata sha'awa a tsakanin su da mazajensu.
Daga na shi bangare shugaban babban asibitin birnin Gaya Docta Inoussa Gwanda, ya bayyana cewa lokaci zuwa lokaci suna samun matan da wannan al'ada ta kaciya ta fada a kansu musamman ma wadanda ke fitowa daga kasashe makofta su na zuwa asibitin domin duba lafiyarsu.
Hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu sun dade suna wayar da kai dan ganin an kawo karshen yi wa mata kaciya. A cewar Barista Adam Aji, alkalin da ke kare kananan yara a mashara'ata ta birnin Gaya akwai dokokin da aka tanada na hukunta duk wadanda kama da laifin yi wa mata kaciya.