1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD na nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Mouhamadou Awal Balarabe
April 19, 2024

Kasashe da dama na duniya da kungiyoyin kasa da kasa sun yi kira da a kai hankali nesa bayan da Isra'ila ta kai harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata

UN Security Council meeting on Iran's attack against Israel
Hoto: Fatih Aktas/Anadolu/picture alliance

Duk da cewa masharhanta na danganta harin daukar fansa da na jeka na yi ka sakamakon rashin tsaurinsa, amma Majalisar Dinkin Duniya na nuna fargaba game da rincabewar yaki a yankin Gabas sakamakon takun saka tsakanin Isra'ila da Iran.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi game da hadarin da ke tattare da takun saka da ya kunno kai tsakanin Isra'ila da Iran. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a birnin New York, babban jami'in ya sake nanata cewa lokaci ya yi da za a dakatar da ramuwar gayya a Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar rikici Zirin Gaza sakamakon mummunan harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila. Guterres ya bayyana cewar irin wannan fito na fito zai iya haddasa rincabewar yaki a Gabas ta Tsakiya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: Yuki Iwamura/AP Photo/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ba da tabbacin cewa Amurka ba ta da hannu a farmakin da Isra'ila ta kai don rama harin da Iran ta kai mata da jiragen yaki marasa matuka. Sai dai takwaransa na Italiya Antonio Tajani ya nunar de cewar Tel Aviv ta sanar da Washington niyyarta ta ramuwar gayya kan Iran, ba tare da Amurka ta amince da wannan yunkuri ko ta shiga an dama da ita ba. Su ma manyan jami'an diflomasiyya na kasashen G7 sun yi kira ga Isra'ila da Iran da su yi kokarin hana ruruta wutar rikicin, yayin da shugabar hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce ya zama wajibi bangarorin sun nisanci matakai da za su haifar da tashin hankali.

Karin Bayani: Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare 300 da jirage marasa matuka

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya mayar da hankali kan hanyoyin kawar da tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya sanar da takunkumin da kasarsa ta aza wa Iran

"Mun himmatu wajen kawo karshen wannan tashin hankalin, kuma kun ga yadda sanarwar kungiyar G7 ta sha alwashin neman karin haske daga Iran. Kuma Amurka ta sanar da karin takunkumi kan Iran, musamman kan tsarin samar da jirage marasa matuka da masana'antar karafa da kamfanonin da ke da alaka da IRGC da ma'aikatar tsaro. Bayanin na G7 ya nunar a fili cewa kasashen G7 za su dauki karin takunkumi ko wasu matakai a cikin kwanaki masu zuwa."

Karin Bayani: Iran ta ce babu wani abin fargaba kan fashewar bam a Isfahan

Tashar makamashin Uranium na Iran a birnin IsfahanHoto: epa/dpa/picture alliance

 Ita kuwa  kasar Sin  ta nemi 'yan kasarta da ke da zama a Iran da su yi taka tsantsa bisa dalilai na tsaro, tare da nuna adawa ga duk wani mataki da ka iya haifar da tashe-tashen hankula tsakanin bangarorin da ke gaba da juna. Sannan fadar mulki ta Beijing ta ce za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalar da ta taso. A nata bangaren, Rasha ta yi alkawarin ci gaba da karfafa gwiwar Isra'ila da Iran domin su kame kansu daga duk wani yunkuri da zai iya mayar da hannun agogo baya a yankin Gabas ta Tsakiya. A wata hira da  ya yi da kafofin watsa labaran kasarsa, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce gwamnatinsu ta yi amfani da musayar yawu da ta yi da jami'an Rasha da Iran cewar ba ta son tashin hankali.  

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi kira ga dukkan bangarorin yankin Gabas ta Tsakiya da su tabbatar da cewa ba a sake samun wani tashin hankali a yankin ba, amma ya ki yin bayani kan harin na ramuwar gayya inda ya ce Jamus za ta tattauna da abokan hulda game da tashin hankali.

Karin Bayani: Kasashen G7 na shirin kakabawa Iran takunkumi saboda Isra'ila

"An sake samun wani farmaki na soja, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. Ba zan iya ba kuma ba zan so in ce wani abu fiye da haka ba. Abu daya da ya fito fili shi ne - ya kamata kowa a yanzu da kuma nan gaba a tabbatar da cewa an kauce wa ci gaban yakin. A matsayinmu na Tarayyar Jamus, tare da abokanmu da Amurka da sauran kasashen G7 tare da abokan aikinmu a Turai , a fili yake wannan shi ne matsayinmu."

Ministan harkokin wajen China Wang Yi da na Saudiyya Faisal bin Farhan Hoto: Murat Gok/Anadolu/picture alliance

Su ma kasashen Larabawa ba a bar su baya wajen tofa albarkacin bakinsu kasar Oman da ke yankin Gulf wacce ta dade tana shiga tsakanin Tehran da kasashen Yamma, ta yi Allah-wadai da harin ramuwar gayya da Isra'ila ta kai wa Iran da ma sauran hare-haren da ta saba kaiwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayyana matukar damuwarta kan ci gaba da zaman dar-dar a yankin, tare da nuna bukatar kamewa domin guje wa hadarin rashin zaman lafiya. A nata bangaren, Masar ta nanata matukar damuwarta game da ci gaba da tabarbarewar dangantaka tsakanin Iran da Isra'ila, inda ta kara da cewa tana kara tuntubar bangarorin da abin ya shafa domin gano bakin zaren warware rashin fahimtar da ke tsakaninsu.

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta yi kira ga Isra'ila da Iran da su guji duk wani matakin da zai fadada rikicin da ake fama da shi. Sai dai Shugaba Recep Tayyip Erodgan ya yi taka-tsan-tsan lokacin da yake bayyana matsayin kasarsa, inda ya ki bayyana kasar da ke da alhakin rikici tsakanin Isra'ila da Iran.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani