1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'An yi watsi da muradun Arewa maso gabashin Najeriya'-MDD

January 22, 2025

Majalisar Dinkin Duniya za ta kaddamar da asusun kudi na kimanin Dala miliyan $910 domin tallafa wa yankin Arewa maso gabashin Najeriya inda kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare tun daga shekara ta 2009.

Wasu mata a sansanin 'yan gudun hijira da ke Pulka a jihar Borno, Nigeria
Wasu mata a sansanin 'yan gudun hijira da ke Pulka a jihar Borno, NigeriaHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa mutane sama da miliyan bakwai ke bukatar daukin gaggawa a jihohi uku da ke shiyyar da suka hadar da Adamawa da Borno da kuma Yobe, duk da cewa MDD ta ce mutum miliyan 3.6 za ta iya bai wa tallafi daga cikin adadin.

Karin bayani: MDD ta yi gargadi kan baraznar yunwa a arewacin Najeriya 

Gabanin wannan ratoho da Reuters ta gani, majalisar ta ce kasashe sun manta da halin da ake ciki a Arewa maso gabashin Najeriya  kasancewar hankalin duniya ya karkata kan Ukraine da Gaza da kuma Sudan.

Karin bayani: Mayakan ISWAP sun halaka manoma sama da 40 a jihar Borno da ke Najeriya

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin cewa manufofin Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan tattalin arziki shi ne ummul-aba'isin jefa 'yan kasar cikin yanayi na damuwa da tsadar rayuwa, sai dai gwamnatin APC ta ce matakin shi ne mafita.