Dusar kankara a kasashen Turai
December 29, 2014Talla
Dusar kankara mai yawan gaske da aka samu tun daga cikin daren jiya Lahadi a tsakanin kasashen Turai ta haifar da rudu da sanya murna a zukatan al'umma da ke zaune a wannan yanki.
Yayin da kimanin mutane dubu 15 ke warwatse a yankunan tsaunika a Faransa cikin wasannin kankara. A Birtaniya yawan dusar kankarar ya haifar daukewar wutar lantarki da zamiyar ababan hawa saboda cikar kankarar a hanyoyin mota a nan Jamus, haka kuma wannan ya haifar da tsaikon ababan sufiri a yankin.
Wani dan Swiss mutum guda ya rasu yayin da wasu talatin suka sami raunika lokacin tafiya a babbar hanya mai tazarar mil 24 daga Ljubljana babban birnin Sloveniya inda kankarar ta zuba sosai a tsakiyar kasar.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu