1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Dusar kankara a Turai ta janyo soke sufurin jiragen sama

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 5, 2025

Yankin kudancin Jamus na daga wuraren da lamarin ya fi kamari, inda aka soke tashin jiragen sama 120 daga cikin 1,090 da aka tsara zirga-zirgarsu a filin jirgin saman Frankfurt.

Filin jirgin saman birnin Frankfurt na Jamus
Hoto: Lando Hass/dpa/picture alliance

Saukar dusar kankara a sassa daban-daban na kasashen nahiyar Turai ta janyo tsaiko da soke zirga-zirgar jiragen sama da na kasa, har ma da motoci, da kuma rufe shaguna da sauran kasuwanni, ciki har da nan Jamus.

Yankin kudancin Jamus na daga wuraren da lamarin ya fi kamari, inda aka soke tashin jiragen sama guda 120 daga cikin 1,090 da aka tsara zirga-zirgarsu a filin jirgin saman Frankfurt, wanda ya fi fice wajen hada-hadar jiragen a Jamus.

Karin bayani:Dusar kankara ta gurgunta harkoki a Jamus

Dusar kankarar ce ta shafe titin sauka da tashin jiragen saman, da ke bukatar kwashewa da kuma samun kyakkyawan yanayin ganin sarari sosai kafin komawa aiki yadda ya kamata.

Haka dai batun yake ga bangaren sufurin jiragen kasa, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Jamus Deutsche Bahn ta sanar.

karin bayani:

Sauran kasashen da dusar kankarar da muku-mukun sanyi suka janyo tsaikon al'amura sun hada Burtaniya da Holland da sauransu, lamarin da tilasta matafiya hakura da tafiye-tafiyen da suka tsara yi a Lahadin nan.

A Burtaniya dai filayen jiragen sama sun soke jigilar fasinjoji da dama a biranen Manchester da Birmingham da Bristol da kuma Liverpool na Ingila, da kuma Cardiff da ke Wales, har ma da jiragen kasa da shaguna da tsayar da sauran harkokin yau da kullum.

Lamarin da ake ganin ka iya janyo dakatar da wasan hamayya na gasar firimiyar Ingila tsakanin Liverpool da Manchester United, ko da ya ke jami'an hukumar kwallon kafar kasar na ci gaba da kai kawo don ganin wasan ya gudana kamar yadda aka tsara a Lahadin nan.

A Holland ma an soke tashin jirage 70 a filin jirgin saman Amsterdam, inda jami'an filin jirgin ke fatan al'amura za su iya daidaita zuwa cikin daren Lahadin nan.