Dusar kankara ta halaka mutane 61 a Afghanistan
January 24, 2026
Talla
Mai magana da yawun Hukumar Bada Agajin Gaggawa, Mr. Parwan shi ne ya tabbatar da hakan kamar yadda ya wallafa a shafin X, ya ce mutane kimani 110 sun samu raunuka, yayin da wasu kimanin 450 suka rasa muhallansu. A jamlace dai dusar kankarar ta shafi mutane kimanin 360.
Hukumomin lardin Bamyan na ci gaba da aike wa da kayan abinci ga mutanen da suka makale a kankara, tare da gargadin mutane da su kaucewa bin titunan da dusar kankarar ta mamaye.