Duterte ya isa kasar Netherlands don fuskantar shari'a a ICC
March 12, 2025
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta tabbatar da isowar jirgin sama da ke dauke da tsohon shugaban Phillipines Rodrigo Duterte a kasar Netherlands, domin fuskantar shari'a bisa zarginsa da aikata laifuffukan yaki da safarar miyagun kwayoyi. Kakakin kotun ICC Fadi El Abdallah ne ya ba da wannan tabbaci ga manema labarai a birnin The Hague, inda ya ce za a fara kai Duterte gidan yari kafin a gurfanar da shi a gaban kotu a cikin kwanaki masu zuwa.
Mista Duterte, mai shekaru 79, ya kasance tsohon shugaban kasar nahiyar Asiya na farko da za a gurfanar a gaban kotun ICC, wacce ta ce akwai kwararran shaidu da ke nuna cewar ya aikata laifin cin zarafin bil'adama da aikata kisan kai a lokacin yakin neman zabe. Sai dai, duk da cewa Philippines ta fice daga ICC a 2019, amma kotun na ci gaba da hukumta kashe-kashen da suka faru kafin janyewar, da kuma wadanda aka aikata a birnin Davao lokacin da Rodrigo Duterte ya kasance magajin gari.