DW za ta je kotu kan hana wakilanta aiki a Habasha
December 13, 2025
Hukumar gudanarwa ta DW ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Habasha ta dauka na dakatar da wakilanta guda biyu daka aikin jarida a fadin kasar na har illa masha Allahu. A wata sanarwar mai kama da martani da DW ta fitar kan hukuncin ranar Juma'a, ta ce Hukumar Yada Labaran Habasha (EMA) ba ta bayar da takamammen dalilan sa wa 'yan jaridar takunkumi ba.
Babbar editan DW Manuela Kasper-Claridge ta ce "Ba abin yarda ba ne, a dakatar da wakilanmu guda biyu daga aikin ba tare da wani takamaiman bayani ba. Ta kara da cewa "Dole mu fara nazarin daukar matakin shari'a cikin wuri" inji Manuela
Babbar editar ta ce al'umma na gamsuwa da rahotannin da wakilan DW ke aikowa daga Habasha "Miliyoyin 'yan Habasha sun dogara da shirye-shiryenmu na harshen Amharic, tare da amincewa mu gabatar da ingantaccen rahoto daga sassan kasar,". Ta tabbatar da cewa ba za ta nade hannu kan wannan mataki ba. "Mun yi watsi da zarge-zargen da hukumar kula da harkokin yada labarai ta Habasha ta yi wa ma'aikatanmu, kuma muna goyon bayan wakilanmu"
DW ta ce a ranar 23 ga watan Oktoba, hukumar kula da yada labaran kasar Habasha ta EMA ta dakatar da wakilan DW guda tara na wani dan lokaci. A cikin wata wasika da ta aike wa DW a ranar Litinin, hukumar ta ce an wanke masu aiko da rahotanni bakwai don ci gaba da aikinsu, yayin da sauran biyun kuma aka dakatar da su na dindindin.
Mutanen biyu dai sun yi ta ba da labarin abubuwan da suka faru a yankin Tigray na kasar Habasha, inda aka kwashe shekaru biyu ana rikici, da kuma Amhara, inda sojojin Habasha suka kwashe shekaru suna fafatawa da 'yan tawaye.
Wasikar ta EMA ta dogara da dakatarwar ne bisa ikirarin "Ci gaba da rashin bin dokokin Habasha da ka'idojin kwarewar aiki," in ji DW, inda ta kara da cewa ta sha yin tambayoyi kan takamaiman koke-koke amma ba ta samu amsa ba.
"Ko da a lokacin da yake bayar da hujjar dakatarwar da aka yi na wucin gadi da aka yi wa dukkan wakilan DW na wucin gadi, mai kula da harkokin yada labarai ya ba da misali da karya ka'idojin watsa labarai guda biyu ne kawai, ba tare da yin la'akari da takamaiman rahoton DW ba," in ji DW a cikin sanarwar.
Har ila yau wasikar EMA ta zargi kungiyar editan Amharic ta DW da ke Bonn da buga "Bayanan da ba su dace ba" da kuma "latsa labarai da bayanai masu hadari." DW ta ce babu wata shaida da ta tabbatar da zargin hukumar EMA.
DW ta ci gaba da cewa "Babu daya daga cikin zarge-zargen da ya dace kuma ta ce za ta yi nazari kan wasu kwakkwaran misalan idan hukumar za ta bayar da su,” in ji sanarwar da babbar tashar DW ta fitar.