1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

dw.com: Sabon tsari, abubuwan da aka sani

Barka da zuwa sabuwar kafar Internet ta DW!

Tare da sake fasalin kafar Internet ta DW da sabunta manhajarmu, yadda kuke samun labaranmu ya canza.

Mun tsara sababbin hanyoyin shiga kafarmu ta Internet, domin saukaka samun labaran DW ta dandamalin digital.

Bayan matakin beta don habaka wa da gwada sabuwar kafar, an rufe tsohon yayi na shafukan DW. Yanzu an bude sababbin shafukan gaba daya.

 

Mene ne sabo?  

A matsayin masu amfani da shafin DW, kune kan gaba a abubuwan da muka yi. Shi ya sa:  

  • Koyaushe tsari daya muka bai wa shafukanmu, ba tare da la'akari da na'urar da kuke amfani da ita don samun su ba.  
  • An inganta shafukanmu domin samunsu a kan wayoyin hannu, „smartphones“ da „tablets“. 
  • Ana gabatar da labaranmu tare da la’akari da ganinsu a cikin hotuna. 
  • Yanzu za ku iya kara sanin 'yan jaridarmu da ke gabatar muku da shirye-shiryenmu.

A halin yanzu, ana ci gaba da bunkasa sababbin shafukan DW. Tuni aka shigar da sababbin abubuwa masu amfani da ban sha'awa! 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW