1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola ta fara ja baya a Laberiya

Salissou BoukariOctober 2, 2014

Shugabar ƙasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf, ta sanar cewar, an fara samun taƙaitar yaɗuwar cutar Ebola a wannan ƙasa da cutar tafi muni.

Ebola Westafrika I.S.A.R. GERMANY Liberia
Hoto: I.S.A.R. GERMANY

A baya-bayan nan dai wani an gano wani mai ɗauke da wannan cuta a ƙasar Amirka wanda kuma ya tafi ƙasar ne daga Laberiya. A wannan Alhamis ɗin ce ake shirya wata babbar mahawara a birnin London, kan cutar ta Ebola da ke ci gaba da addabar wasu ƙasashen yammacin Afirka da suka da Saliyo, da Gini sai kuma Laberiya inda aƙalla mutun biyar ke kamuwa da cutar a kowace awa a cewar Ƙungiyar Save the Children.

A wani jawabi da ta yi kan wannan batu na Ebola, shugabar ƙasar ta Laberiya, ta ce a halin yanzu an fara taƙaitar yaɗuwar cutar, sannan kuma an fara samun ragewar masu zuwa asibitoci. Kasar ta Laberiya dai ta samu aƙalla mutane 1.998 da suka rasu, daga cikin 3.696 da suka kamu da cutar ta Ebola.