Ebola ta kashe sama da mutane 5,000 a Kwango
October 31, 2026
Talla
Ana ganin har yanzu akwai sauran aiki kan hukumomi na shawo cutar, wadda ta zama mafi muni wajen yawan mace-mace a tarihin barkewarta a kasar. A watan mayun wannan shekarar ce dai cutar ta barke a Kwango, inda sama da mutane 10,000 sun kamu da ita. Jami'an lafiya sun ce jinkirin gano cutar da rikice-rikice da matsin lamba kan ayyukan kiwon lafiya sun taimaka wajen saurin yaduwarta.
Karin bayani: An fara rigakafin Ebola a Kwango
Barkewarta a wannan lokacin na zama mafi muni a karo na biyu a duniya. Inda ta yadu a yammacin Afirka tsakanin shekarun 2014 da 2016 ce kadai ta fi ta girma.