Ebola ta sake ɓulla a Saliyio
April 7, 2015Talla
Tun can da farko gwamnatin ta ba da sanarwar cewar an kakape cutar daga yakin bayan da aka shafe watanni uku babu wani sabon kamuwa da cutar. Gwamnatin ta Saliyio ta ce ta killace iyaye da kuma na kusa da jaririn, sannan Ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ta ce ta aike da wata tawaga domin tanttance dukkanin mutane da suka yi hulɗa da jaririn.
Hakan kuwa na zuwa ne a daidai da ake gudanar bukukuwan ranar kiwon lafiya ta duniya a yau bakwai ga watan Afrilu. Kawo yanzu, cutar ta Ebola wacce ta fara bazuwa a Gini a shekarun 2013 kafin ta isa a Laberiya da Saliyion,ta kashe sama da mutane dubu goma a cikin ƙasashen uku na yankin yammacin Afirka.