Lafiya
Ebola ta sake ta'azzara a Congo
July 31, 2026
Talla
Adadin ya zarce yawan wadanda suka kamu a annobar da ta fi muni tsakanin shekarun 2018 da 2020.
Alkaluma sun nuna cewa mutane 1,556sun mutu kawo yanzu, yayin da annobar ke ci gaba da yaduwa musamman a lardin Ituri da ke gabashin kasar, yankin da ya dade yana fama da rikice-rikice.
Karin bayani : Ya za a shawo kan matsalar Ebola a Kwango?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu babu ingantacciyar allurar rigakafi ko maganin nau'in cutar Ebolan da ya bulla a Congo, sai dai ana ci gaba da gwaje-gwajen sabbin alluran rigakafi domin dakile yaduwarta.