Ebrahim Raisi ya lashe zaben shugaban kasa a Iran
June 19, 2021Dan takarar shugabancin Iran mai matsakaicin ra'ayi Abdolnasser Hemmati ya taya abokin hamayyarsa mai ra'ayin mazan jiya Ebrahim Raisi murnar lashe zabe, sa'o'i kalilan bayan kammala kada kuri'a. Cikin wata wasika da kafofin watsa labaran Iran suka ruwaito, tsohon shugaban babban bankin Kasar wato Hemmati ya yi wa Raisi fatan cewa gwamnatinsa za ta kawo ci-gaba ga al'umma.
A wannan asabar ne aka bayar da cikakken sakamakon zaben shugaban kasa a Iran bayan da aka shafe sa'o'i 19 ana kada kuri'a. Hukumomin kasar sun tsawaita lokucin gudanar da zaben ne sakamakon matakan hana yaduwar cutar corona da ke kawo tsaiko wajen gudanar da aikin zabe yadda ya kamata.
Dama dai dan takara Ebrahim Raisi da ya sami amincewar shugaban addini na kasar ta Iran Ayatollah Ali Khamenei ne ake sa ran zai lashe zaben. Shi dai Raisi mai shekaru 60 da haihuwa ya fara shiga takarar zaben shugaban kasa na 2017, inda ya sha kaye a hannun mai matsakaicin ra'ayin siyasi Hassan Rohani, wanda ba shi damar sake tsayawa takara bayan wa’adi biyu na shugabanci kasa.