1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: Bukatar daukar mataki kan masu juyin mulki

Uwais Abubakar Idris
October 4, 2022

Majalisar dokokin kungiyar ECOWAS ta bukaci daukar mataki a kan masu juyin mulki da ke kawo tsaiko ga mulkin dimukurdiyya. Kungiyar ta yi tir da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso

Taron kolin kungiyar ECOWAS
Shugaban Senegal Macky Sall da na Togo Faure Gnassingbe a taron ECOWASHoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Majalisar dokokin ta baiyana bukatar hanzarta daukar matakan ladabtarwa da ma kaste hanzarin masu yin mulki da sannu a hankali ke kara yin kuste ga mulkin dimukurdiyya a kasashen Afrika ta yamma domin zama darashi ga na baya. Jonathan Kaipah dan majalisar dokokin ECOWAS ne daga kasar Liberia yace dole su yi amfani da sandar da ke hannunsu.

Sojojin juyin mulki a Burkina Faso Hoto: Radiodiffusion Télévision du Burkina/AFP

‘’Yace ya kamata mu yi amfani da karfin ikon da muke da shi a hannunmu don shawo kan wannan matsala, wannan zai mana sauki a kan tafiyar da sauran al'amura da ma matsaloli da ke fuskantar nahiyar Afrika. Ba zai yiwu mu sanya idannu ba al’amura na tafiya haka, ta haka ne zamu iya samar da ci gaba a yankin’’.

Masharhanta na bayyana cewa rashin daukar tsauraran matakai a kan masu juyin mulki, na kara bude kafa ne kawai ga tsagerun sojoji da ke amfani da karfin bindiga wajen kifar da gwamnatin dimukurdiyya. Majalisar dokokin ta ECOWAS dai ta yi Allah wadai da lamarin. Hon Mansur Ali Mashi dan majalisar ne.

Halin da ake ciki a Burkina FasoHoto: Vincent Bado/REUTERS

"Sannu a hanakali dai ana kara fuskantar karuwar juyin mulki a kasashen Afrika ta yamma, domin kama daga kasar Mali zuwa Guinea Conakry da ma Burkin Faso dukkaninsu sojoji ne ke mulki da karfin bindiga".

Dr Faruq BB Faruq masanin kimiyyar siyasa da ke jami’ar Abuja ya bayyana hadarin da ke tattare da wannan.

Ga Hon Sidie Mohammed shugaban majalisar dokokin ECOWAS din yace dole majalisar ta kara kaimi a kan kasashe musamman wadanda ke shirin gudanar da zabe don tabbatar da dorewar mulkin dimukurdiyya.

A lokutan baya dai tsawatarwa da yin Allah wadai da kungiyoyin yankin Afrika na ECOWAS da ma ta Majalisar Dinkin Duniya kan kasa yin tasiri.

Kungiyar ECOWAS dai na shirin gudanar da taron don tattauna wannan batu na kasar Burkina Faso da ke neman zama sabon yayi a kasashen yankin Afrika ta Yamma

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani