1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS: Bukatar hadin kai wajen dawo da martabar kungiyar

February 8, 2024

ECOWAS ta bayyana kaduwa game da rikita-rikitar da ake fuskanta a Nijar da Mali da Burkina da kuma Senegal tun bayan da shugaba Macky Sall, ya dage zabe, da matakin ya sake bude sabon babin siyasa a yammacin Afrika.

Shedikwatar ECOWAS Abuja, Najeriya
Shedikwatar ECOWAS Abuja, NajeriyaHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban hukumar zartaswar ECOWAS Omar Alieu Touray ya bayyana yanayi da kungiyar ke ciki a matsayin babban kalubale, inda ya bayyana rikicin siyasar Senegal a matsayin dambarwa mafi ta da hankali.

Wannan bayyana kaduwar ya fito fili a ne a taron da ministocin harkokin waje na kasashen yammacin Afrika suka gudanar a Abuja kan dambarwar siyasar Senegal da kuma ficewar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar ECOWAS.

Wannan yanayi da ake ciki a yammacin Afrika, lokaci ne da ya kamata kasashen su hada kawunansu wajen jaddada dimukradiyya, kamar yadda Touray, ya sanar da hakan a Abuja na tarayyar Najeriya.

Ministocin tsaro da harkokin kasashen waje na Senegal sun halarci taron, amma ba a ga fuskokin wakilan kasashen Mali da Jamhuriyar da kuma Burkina Faso ba da kungiyar ta sallama daga cikinta sakamakon juyin mulki, wanda daga bisani suka sanar da dankwafar da shahadar kasancewa a cikin kungiyar.