1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS: Burkina Faso ta sanar da ficewa a hukumance

January 30, 2024

Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya ga kwafin wasikar da Burkina Faso ta aikewa ECOWAS na bukatar ficewa daga cikin kungiyar da ta kasance rumfa ga kasashe mambobinta.

Hoto: Nipah Dennis/AFP

Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun bi sahun Mali wajen mika takardar bukatar ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS a hukumance.

Tun da fari dai ma'aikatun harkokin wajen Mali da Nijar suka mika bukatar ficewa daga ECOWAS tun daga ranar 29 ga watan Janairu 2024.

Kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga kungiyar ta ECOWAS a ranar lahadin da ta gabata ta kafar talabijin a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.

Matakin na kasashen uku ya biyo bayan takun-saka da ke tsakanin su da kungiyar ta ECOWAS tun bayan hambarar da gwamnatocin farar hula a lokuta daban-daban.