1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da shinkafa a yammacin Afirka

December 17, 2021

Shugabannin kungiyoyin manoman shinkafa na yammacin Afirka, sun gana a Abuja fadar gwamnatin Najeriya da nufin aiki tare wajen wadatar da daukacin yankin da shinkafar.

Nigeria Kebbi | Überschwemmung zerstört Ernte
Ambaliya na daga cikin kalubalen da manoman shinkafa ke fuskanta a NajeriyaHoto: DW

A baya dai yankin na ECOWAS ko CEDEAO, na zaman na kan gaba wajen shigo da shinkafar daga kasashen gabashin Asiya. Kuma a tsakanin Tarayyar Najeriya ya zuwa Jamhuriyar Benin dai, kasashen biyu ya zuwa shekarar 2017 na shigo da kaso 50 cikin 100 na daukacin shinkafar da ake ci a yankin Kudu da Hamadar Sahara ta nahiyar Afirka. Wani kamfe na gwamnatin Najeriyar ne dai, ya sauya mata matsayi daga ta farko a shigowa da shinkafar ya zuwa ta kan gaba cikin noma da sarrafata a daukacin kasashen nahiyar Afirkan.

Karin Bayani: Najeriya na fuskantar barazanar yunwa

Nasarar kamfen din kuma na shirin haifar da wani tsari na hadin gwiwa a yankin yammacin Afirkan da ke neman hadewa wuri guda, domin yin aiki tare wajen noman shinkafar. Wani taro na shugabannin manoman shinkafa na kasashen yankin 15 dai, na kokarin nazarin nasarar Najeriyar da kuma maimaita ta a daukacin kasashen yankin. Madam Halimatou Len na zaman shugabar masu neman shukafar a kasar Senegal: "Mun saurari kafafen labarai, kuma mun ji yadda aka samu sauyi mai inganci ga batun noman shinkafa. Mun zo mu gani da idanunmu, na kuma gamsu da abin da na gani tun sauka ta a Najeriya da kuma abin da naji wajen mahukunta. Muna tunanin aiki tare, kuma abin da muka gani a Najeriyar ya burge mu."

Mata da dama na mayar da hankali wajen noma shinkafa a AfirkaHoto: AP

Tun bayan kaddamar da sabon shirin na ci da kai da ke zaman babban kwazo shekaru shida baya, yawan shinkafar da kasar ke nomawa da kuma casawa a kamfanoni ya karu da kusan kaso 26 cikin 100. A bana kadai dai kasar ta casa tan miliyan biyar na shinkafa, a cikin tan miliyan kusan takwas da ta noma sakamakon karuwar kamfanonin casar shinkafar. Ahmed Mohammed Dukku na zaman wakilin kungiyar manoman shinkafar, kuma ya ce Najeriyar tana shirin koyar da dabarun nasarar tata ga ragowar kasashen yankin. Tuni dai aka fara gwada hadakar, inda manoman Najeriyar ke tsallakawa zuwa makwabciya Jamhuriyar Benin domin gwada noman shinkafar a cikin burin hada kan da ke zaman alamun nasarar gamayyar yankin da ya amince ya bude dukkan iyakokinsa daga farkon watan Janairun gobe.

Karin Bayani: Masara ta bi sawun shinkafa a Najeriya

A fadar Aminu Goronyo da ke zaman shugaban kungiyar manoman shinkafar Najeriyar, bangarorin dai na duban yiwuwar bude cinikin shinkafar a tsakanin daukacin kasashen yankin 15. Wadatar da abinci tsakanin al'ummar ECOWAS ko CEDEAO din kusan miliyan 400 dai, ka iya taimakon yankin ga batun ciniki mara shinge ko bayan rage dogaro da kasashen Asiya da suka dauki lokaci suna mayar da yankin matattarar gurbatacciyar hajar shinkafar.