1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS/CEDEAO ta cika shekaru 50 da kafuwa

Mansur Bala Bello Suleiman Babayo
May 28, 2025

Shugabannin kasashe na kungiyar ECOWAS/CEDEOA suna taro a birnin Lagos na Najeriya kan bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, inda ake duba kalubalen da take fuskanta.

Taron Shugabannin kasashe na kungiyar ECOWAS/CEDEOA
Taron Shugabannin kasashe na kungiyar ECOWAS/CEDEOAHoto: Ubale Musa/DW

Kungiyar ta ECOWAS/CEDEOA tana bikin lokacin ta kasashen yankin na yammacin Afirka suke cikin kalubale kan kudin fito na kayayyakin da ake kai wa zuwa kasar Amurka da kuma janye tallafin kasashen duniya da gwamnatin kasar ta yi. Kana kasashe uku na kungiyar Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar da sojoji suka kwace madafun iko sun fice daga cikin kungiyar a farkon wannan shekara.

Karin Bayani: Wakilan Kungiyar AES na tattaunawa kan manufofin kungiyar

Taron Shugabannin kasashe na kungiyar ECOWAS/CEDEOAHoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS suna fama da kalubalen tsaro na kungiyoyin masu ikirarin jihadi. Kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin sun fuskanci hare-haren tsageru masu kaifin kishin addinin Islama cikin wtaannin da suka gabata. Kana juye-juyen mulkin soja irin wanda aka gani a kasashen uku (Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar) da suka fice daga cikin kungiyar.

Daga cikin shugabannin kasashen na ECOWAS da suka saka hannu wajen kafa kungiyar shekaru 50 da suka gabata, tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon mai ritaya ne kadai ya rage a raye, wanda yake da shekaru 90 da haihuwa.