Kafa rundunar shirin ko-ta-kwana a Nijar
August 10, 2023Talla
Matakin na kunshe cikin sanarwar bayan taron da kungiyar ta Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, ta kammala a Abuja fadar gwamnatin Najeriya. Kungiyar ta ce ta dauke wannan matakin ne, bayan duk wani yunkuri na shawo kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din ya ci tura. Tun da fari a jawabinsa na kammala taron shugaban Najeriya kana jagoran kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, babu wani mataki da kungiyar ba za ta dauka ba har da amfani da karfin soja da suke fatan ya zama mataki na karshe.