ECOWAS ta kasa cimma matsaya kan Mali Gini da Burkina Faso
June 5, 2022A ka'idance a taron kolinsu da aka kammala a yammacin jiya a birnin Accra, ECOWAS za ta duba yiwuwar daukar wasu kwararan matakai ne ko akasin haka, game da sojojin da suka kifar da gwamnatocin fararen hula a kasashen yankin uku, sai dai daga bisani an dage matakan har sai uku ga watan gobe bisa rashin cimma matsaya daya na kara matakan ladaftarwa ko sassauto da su.
Wata majiya da ta so a sakaye sunanta, ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai an AFP cewa duk da kebewa ta sirrin da suka yi a tsakaninsu, shugabannin sun kasa jituwa game da matakan da ya dace su shata wa sojojin da suka yi juyin mulki.
Mali da ke takon saka da kungiyar ta sanar da bukatar shriya zabe nan da watanni 24, a yayin da sojan Burkina Faso suka shata wa kansu wa'adin shekaru uku na mulki, a nata bangare ita kuwa kasar Guinea Conkry sojojin suka ce za su kasance kan iko har tsawon watanni 36, lamarin da ECOWAS ta ce sun saba wa ka'idodinta.