1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: ECOWAS za ta sake shiga tsakani

August 20, 2020

Shugabannin kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma Ecowas, sun kamalla wani taro kan juyin mulkin Mali, inda suka ce za su tattaunawa da masu ruwa da tsaki a rikicin, koda yake sun saka mata takunkumi.

Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen
Taron shugabannin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a AbujaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Bayan share tsawon kusan sa'o'i hudu ana tattaunawa, shugabannin kasashen kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Afirka ta Yamman wato Ecowa ko CEDEAO, sun ce suna shirin bude tattaunawa da daukacin masu ruwa da tsaki a cikin rikicin Malin ne, a wani mataki na kokarin sake mayar da dimukuradiyyar kasar bisa turba. Wata sanarwar bayan taron da suka gudanar a Abuja dai, ta kuma jaddada neman sakin hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita da daukacin daurarrun rikicin.

Tilas a matsa lamba ga sojoji

Sanarwar dai ta ce Malin a karkashin sojan za ta ci gaba da fuskantar takunkumi na tattalin arziki da ma huldar diplomassiyya da daukacin kasashen yankin, in ban da bukata ta abinci da magunguna da makamashin man fetur da al'ummar kasar ke da bukata da nufin rayuwa ta yau da ta gobe.

Zanga-zanga a Mali ta sanya sojoji sun yi juyin mulkiHoto: picture-alliance/dpa/M. Salaha

Daukacin shugabannin yankin dai na kallon juyin mulkin Malin a matsayin barazanar tsaro da zaman lafiya ga daukacin yankin na yammacin Afirka. Abun kuma da a cewar shugaban Najeriyar Muhammad Buhari ya sa matsa lamba ga sojojin Malin ke zaman wajibi. Duk da cewar dai tun a ranar Larabar da ta gabata, kasashen yankin sun fara tunanin karfi na hatsi a matsayin hanyar kai karshen takkadamar, taron ya kare da karkata zuwa kare kasar da ya ce sojan na yammacin Afirka za su tabbatar da hadin kan sojojin Majalisar Dinkin Duniya 15,000 da kungiyar G5 ta kasashen yankin Sahel da Faransa da ke kasar a halin yanzu.

Ana dai saran sojojin kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO din, za su bayar da kariya ga kadarori na kasar, baya ga zama matakin farko na tsaro ga kasar da ta dauki lokaci tana fama a cikin annoba ta ta'adda. Har ya zuwa juyin mulkin wannan mako dai, mafi yawa na kasar Malin na hannun kungiyoyin ta'adda da ke cin karensu har gashinsa da kuma ake ta'allaka tasirinsu da kare gwamnatin ta Keita da ke cikin wa'adin mulki na biyu.

Hambararren shugaban Mali Boubacar KeitaHoto: ORTM/Reuters

Abun kuma da ya jefa shugabannin yankin cikin tsaka mai wuya tsakanin goyon baya ga gwamnatin da 'yan kasar ba sa rakiya da kuma kyale mulkin sojan da ke zaman aiken sako mara kyau a daukaci na yankin, abun kuma da ga dukkan alamu ya tilasta kara fadada tattaunawa ya zuwa kungiyar Tarayyar Afirka ta AU. 

Shirin sake tura jakadu

Taron  dai ya amince da sake aika manzo na musamman na kasashen, kuma tsohon shugaban Najeriyar Goodluck Ebele Jonathan da kuma shugaban kungiyar ECOWAS din Jean Kassi Brou ke zana 'yan sakon, da za su share fage na bude tattaunawar mai tasiri. To sai dai kuma ko zuwa ina ake shirin a kai da nufin sabon lallashi ga sojan da suka bayyana aniyarsu ta sabon zabe cikin lokaci kalilan, ga Auwal musa rafsanjani da ke zaman tsohon sakataren hadin gwiwa na  kungiyoyi na fararen hula a yankin yammacin Afirkan, akwai alamu na gazawa na shugabannin yankin ga kare muradun al'ummarsu. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin kare shugabanni komai runtsi da kuma kare muradun al'ummar yankin.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani