Rufe iyakokin Najeriya cikas ne ga Ecowas
February 16, 2020Talla
Taron wanda ya hada ministocin harkokin waje da na kasuwanci na kungiyar Ecowas, ya yi tsokaci a game da matakin na rufe iyakokin da Najeriya ta yi wadanda suka ce ya sabama yarjejeniyar kasuwanci da ke a tsakanin kasashen. A cikin watan Augusta ne gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta saboda dalilan da ta kira na dakatar da fasa kobri na shigo da shinkafa da kuma kaji da ta ce ake shigomata da su daga Jamhuriyar Benin.