SiyasaAfirka
ECOWAS ba za ta yi watsi da Burkina Faso ba
March 18, 2022Talla
Ministan harkokin wajen kasar Ghana Shirley Ayorkor Botchway da kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta tura Burkina Faso ta ce ECOWAS za ta ci gaba da aiki kafa-da-kafa da gwamnatin sojin Burkina faso, duk da fargabar da ake yi ta sojoji za su tsawaita zamansu a mulki har nan da shekaru uku.
A yayin da jami'in diflomasiyyar ke magana a ranar Alhamis a birnin Ouagadougou ya ce ECOWAS ta damu a kan tsawaita zaman sojojin kan mulki amma sojojin da suka yi juyin mulki a watan Janairun da ya gabata sun yi mata cikakken bayani a game da dalilansu na yin hakan. Kuma halin da kasar ke ciki ba lokaci ne da ECOWAS za ta yi watsi da ita ba.