1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS: Neman mafita ga rikicin siyasar Senegal

February 12, 2024

A cigaba da kokarin samun mafitar rikicin siyasa a kasar Senegal, kungiyar ECOWAS ta aike da tawaga zuwa Dakar don ganawa da shugabannin kasar da ke fuskantar sabon rikicin siyasa a cikin gida

Nigeria | ECOWAS-Staatsoberhäupter in Abuja 2023 | Regionale Zusammenarbeit
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

An dai tsara shugaban ECOWAS din Bola Ahmed Tinubu zai isa birnin Dakar da nufin bude tattaunawa cikin sabuwar takkadamnar da ke neman yamutsa hazo a kasar Senegal kafin kuma babu zato ba tsamanni kungiyar sauya matsayi ta tura wata tawagar yan majalisar kasashen yankin a karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin ECOWAS din Dr Sidie Mohammed Tunis domin ganawar da ke zaman irinta ta farko a tsakanin mahukuntan Sengal din da kuma kungiyar da ke cikin rudani.

Taron wakilan kungiyar ECOWAS a Abuja NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Tawagar dai a fadar sanarwar ECOWAS din za ta yi ganawa da daukacin 'yan siyasar kasar da kungiyoyin farar hula da nufin kwantar da hankula a cikin kasar. Wannan ne dai karo na farkon da kungiyar ke tura wakilci cikin kasar tun bayan dage zabe da shugaban kasar Macky Sall ya yi.

Karin BayaniECOWAS: Bukatar hadin kai wajen dawo da martaba

Sabon matsayin dai na kama da sauyin taku a tsakanin kasashen yankin da ke cikin yanayi maras tabbas tun bayan ficewar kasashen Mali da Niger da Burkina.

ECOWAS din kuma a fadar Dr Kabir Sufi kwararren masani kan siyasar yankin ta dau lalalshi da nufin kaucewa kara kirga asarar da ke da zafin gaske.

Hoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Dama dai an dauki lokaci ana kallon shugabancin ECOWAS da daure gindi ga masu kokarin zarcewa kan karagar mulki a yayin da ya ke barazana ga sojin yankin.

Kuma tun daga kau da kai cikin karin wa'adin a Guinea, ya zuwa tsawaitar wa'adin a kasar Togo dama kokarin sauya kundin tsarin mulkin Mali, ko in kular ECOWAS na zaman ummul haba'isin rigingimun siyasar da ke zaman ruwan dare game duniya a kasashen yankin yanzu haka.

Karin Bayani: AU ta nemi Senegal ta gaggauta gudanar da zaben shugaban kasa

Faruk BB Faruk mai sharhi ne kan siyasar yankin, kuma ya ce akwai babban rashin fahimta a tsakanin shugabannin kasashen ECOWAS bisa manufar kafa kungiyar tun daga farko

Dole da ke kama da kanwar naki, ko kuma neman mafitar rikici irin na gadon gado, akwai dai tsoron rigingimun na siyasa na iya kaiwa ya zuwa tasiri ga batun tsaro da kila kasuwancin yankin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani