Fatan sasanta rikicin Nijar da ECOWAS
August 24, 2023Duk da cewar dai cikin bukata ta kashin kai ne dai, Malaman Addinin Islamar na Najeriyar suka fara tattaunawa da nufin kaucewa karfin rikicin juyin mulkin na Jamhuriyar Nijar. To sai dai kuma sannu a hankali, suna shirin sauya da dama cikin neman sake mai da Nijar din kan turbar dimukuradiyya ta hanyar sulhu. Kuma bayan ganawa ta tsawon kusan sa'o'i biyu dai, shugaban Tarayyar Najeriyar kuma jagoran kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO Bola Ahmed Tinubu ya nemi malaman su koma Nijar da nufin ci gaba da tattauna batun neman mafita. Majiyoyin zauren taron dai sun ce, malaman sun yi nasarar sassauto da sojojin Jamhuriyar Nijar din daga dokin shekaru ukun da suka hau kai suka zauna.
Duk da cewar dai babu bayanai dalla-dalla kan bukatun sojojin Nijar din, akwai yiwuwar rage tsawon lokacin da za su sake mika mulki ga gwamnatin dimukuradiyya da kila ma makomar shugaban kasar da ke hannunsu. Kokari na neman mafita ko kuma taunin tsakuwa a cikin neman bai wa aya tsoro dai, daga dukkan alamu kama daga sojojin Nijar din ya zuwa ga ita kanta Abujar sun yi nisa a cikin batun samun sulhu. Asarar shugaban sojojin hayar Wagner dai, ka iya dusashe duk wani fatan sojojin da suka yi juyin mulkin Nijar din na iya tunkarar rundunar ko-ta-kwanan da ECOWAS ta ce za ta tanada. A hannu guda kuma daukacin kasashen yankin, na fuskantar rashin kudi da ma yanayin siyasar da ke iya ba su damar kai yaki zuwa Yamai.