ECOWAS ta cire takunkumi a kan kasar Mali
October 6, 2020A cikin watan sanarwa, kungiyar ta ce shugabannin kasashe da gwamnatoci mambobinta sun yanke shawarar dage takunkumin ne bayan yin la'akari da kyakkyawan mataki da kasar ta dauka na kama hanyar mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya tare da wallafa jadawalin komawa ga mulkin farar hula.
Kungiyar mai mambobin kasashe 15 ta sanya wa kasar Mali takunkumi ne bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita sakamaon zanga zangar gama gari da aka yi ta yi a sassa dama na kasar.
A waje guda kuma an sako madugun adawa a kasar Malin Soumalia Cisse da masu kaifin kishin Islama suka yi garkuwa da shi tsawon watanni shidda yayin yake yakin neman zabe da kuma wata jami'ar agaji ta kasar Faransa wadda ita ma aka yi garkuwa da ita tun shekarar 2016.