1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta dakatar da kasar Guinea-Bissau

November 28, 2025

A wani mataki na matsin lamba kan sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea Bissau, shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS sun dakatar da kasar har sai ta koma kan tsarin dimukuraddiya

Taron shugabannin ECOWAS a Abuja, Najeriya
Taron shugabannin ECOWAS a Abuja, NajeriyaHoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Ya zuwa yanzu dai daya a cikin uku na daukacin kasashen ECOWAS 15 dai na karkashin mulkin soja. Damuwa mai girma kuma sakon da ke damunin gaske, a tsakanin shugabannin yankin da kila ma kawayen yamma da ke kallom rushewar tsarin dimukuradiyyar ECOWAS. Tuni dai shugabannin yankin suka kamalla wata ganawa tare da ayyana dakatar da kasar ta Guinea Bissau da ke zaman sabuwar amaryar sojan. To sai dai kuma can a zuciyar shugabannin yankin, daga dukkan alamu, gaba na ta faduwa bisa matakin,da ke iya kaiwa ga matsi kan mutanen na Bissau.

Karin Bayani: Senegal ta ba wa hambararren shugaban Guinea-Bissau mafaka

Shugabannin kungiyar ECOWAS ko CEDEAOHoto: Ubale Musa/DW

Duk da cewar dai akasin Nijar, can a Bissau an saki habararren shugaban kasar, tare da rakiyarsa zuwa makwabciya kasar Senegal. Ko bayan kyale masu sa ido na kasashen waje su fice su bar kasar duk da juyin mulkin, a wani abun da ke zaman alamun sassauci a bangaren sabbabin yan mulkin na Bissau. Da kamar wuya matsin kungiyar kasashen ECOWAS ya yi tasiri a tunanin Farfesa Kamilu Sani Fage da ke zaman kwarrare a siyasar yankin. Wata sanarwar bayan taro ta shugabannin yankin dai tun da farkon fari ta ce Guinea Bissau din za ta ci gaba da zama saniya ware har ya zuwa komawarta zuwa tsarin dimukuradiyyar yamma. Sanarwar da ta nada shugaban kasar Togo Faure Gnassimbe domin jagorantar wata tawagar sassantawa ta shugabannin yankin, dai ta ce sojojin na Bissau ba su da zabi face komawa bisa tsohon tsarin dimukuradiyyar yamman. Ambassada Usman Aliyu dai na zaman tsohon jami‘in diflomasiyar tarayyar Najeriya, ya ce ana bukatar nazari a cikin dokokin kungiyar‚‘‘Koma zuwa ina take iya kaiwa a tsakanin masu kokarin yin boren, da kuma musamman tabbatar da tsarin yamma.

Karin Bayani: Guinea-Bissau: Wa ya kitsa juyin mulkin soja?

Janar Horta N'Tam sabpon shugaban riko na Guinea Bissau tare da mukarrabansaHoto: Patrick Meinhardt/AFP

An dai dauki lokaci ana ta korafi bisa dimukuradiyyar da ke kasashen ECOWAS. Dimukuradiyyar kuma da ta gaza warware batu na talauci a tsakanin miliyoyin al'ummar yankin. Dr Kabiru Sufi dai na bin diddigin siyasar yankin, kuma ya ce ana bukatar kara babban nazari bisa dimukuradiyyar ECOWAS bayan kallon ruruwar mulkin soja. Ana dai ta‘allaka karuwar talauci dama rashin tsaron da ke a kasashen yankin da gurguncewar dimukuradiyyar ECOWAS da ta bada kafar halin bera da kokarin murde wuya a bangare na shugabannin yankin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW