1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: ECOWAS ko CEDEAO ta gaza

July 20, 2020

Kawancen 'yan adawa a Mali ya yi fatali da shawarwarin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta gabatar, da nufin shawo kan rikicin siyasar kasar.

Bildkombo Mali-Krise
Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kuma Imam Mahmoud Dicko jagoran adawa da shugaban kasa

Tawagar dai ta shafe tsawon kwanaki tana ganawa da bangarorin da ke da ruwa da tsaki, domin warware sarkakiyar, sai dai abin ya ci tura. ECOWAS ko kuma CEDEAO din ai, ta kara tsawaita wa'adin aikinta na sa'o'i 24 a Mali, biyo bayan kasa shawo kan gwamnati da 'yan adawa da ke rikici da juna. A wata sanarwar da kungiyar ta Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamman, wato ECOWAS ko CEDEAO ta fitar a karshen mako, ta bukaci a sake mambobin kotun tsarin mulki da duba sakamakon zaben 'yan majalisa da kuma kafa wata gwamnatin hadin kan kasa, inda bangaren ma su rinjaye za su samu wakilicin mutane 50 da 30 dag 'yan adawa kana 20 daga bangaren kungiyoyin fararen hula. Sai dai tawagar masu shiga tsakanin ta kauce wa duk wani batu na marabus din shugaban kasarIbrahim Boubacar Keïta kafin kammala wa'adin mulkinsa a shekarar 2023.
Jean Claude Kassi Brou shi ne shugaban hukumar ECOWAS ko CEDEAO: "Wannan wani jan layi ne da ba mu da hurumin ketawa domin kasar na karkashin jagorancin kundin tsarin mulki, ya kamata a yi masa biyayya wanda hakan shi ne makullin bude duk wata kofa. Kundin tsarin mulki ya tanadi wa'adin mulkin shugaban kasa da aka zaba na tsawon shekaru biyar, saboda haka mu dole ne mu kiyaye, ba za mu bi duk wani abin da ya shafi mika mulki a wata hanyar da kundin tsarin mulki bai tanada ba, wannan batun ya fi komai, haka kuma muka gayawa 'yan adawa su kuma sun fito fili sun fada mana tasu gaskiyar."

Zanga-zangar adawa da shugaban mali Hoto: Reuters/M. Rosier

Ba wani abin mamaki ba ne da kawancen 'yan adawa ya yi fatali da bukatar ta kungiyar CEDEAO, tare da jadadda matsayinsu na ganin shugaba IBK yayi marabus daga mukaminsa domin kafa gwamnatin ta rikon kwarya wacce suka ce za ta kasance karkashin tubali na dimukuradiyya. Kana ko baya ga hakan, 'yan adawa na bukatar ganin an yi gagarumin bincike game da hare-haren ranar 10 da 11 da ma 12 ga watan Yuli in ji  Mohamed Assaley Ag Ibrahim mamba a kawancen na M5. Sanarwar bayan taron da tawagar masu shiga tsakani ta kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta fitar dai ta bayyana cewa idan har bangarorin sun amince da shawarwarinta na shiga tsakani domin warware takaddamar, za a fara aiki da su ne a ranar 31 ga wannan watan na Yuli da muke ciki.