1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS ta ja hankalin kasashen AES kan ficewa daga kungiyar

May 2, 2024

Majalisar dattijan ECOWAS ta bukaci kasashen Burkina Faso da Nijar da Mali da su sake yin nazari kan matakin da suka dauka na ficewa daga cikin Kungiyar.

Ghana Symbolbild ECOWAS Fahnen
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Majalisar dattijan ECOWAS ko kuma CEDEAO ta kammala taron kwanaki biyu a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire kan rayuwar kungiyar da kuma dambarwar da ake fama da ita a yankin yammacin Afrika. 

A cikin sanarwar ta biyo bayan taron shugaban majalisar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonatan ya bayyana damuwa a game da matakin kasashen yankin Sahel uku da ke karkashin mulkin sojoji da suka hadar da Burkina Faso da Nijar da Mali na raba gari da kungiyar.

Karin bayani: Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun yi bankwana da ECOWAS

Kazalika majalisar dattijan ta tabo batun katsalandan da wasu manyan kasashe ke yi a yankin yammacin Afrika, da kuma raunin kasashen kungiyar, tare da yin kira ga hukumar gudanarwar ECOWAS da ta dauki matakin gaggawa don hana yankin zama fagen yada rikice-rikice kan manufofin siyasa na kasa da kasa.

Karin bayani: ECOWAS: Bukatar hadin kai wajen dawo da martaba

Kasashen uku da ke yankin Sahel dai sun kafa wata kungiya da ake wa lakabi da AES tare da kulla alaka da Rasha bayan korar sojojin Faransa da ke zama uwar gijiyarsu a shekarun baya.