1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta kakaba wa kasar Mali sabbin takunkumai

January 11, 2022

Kasashen yammacin Afirka, sun yanke shawarar kakaba wa Mali karin takunkumai saboda janye shirin zaben watan Fabrairu da sojojin juyin mulki suka yi, matakin da tuni sojojin suka yi tir da shi.

Accra Ghana | Shugabannin kungiyar ECOWAS
Hoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Kasashen na yammacin Afirka dai sun ce za su tsananta wa Malin ne ta fuskatar rufe iyakoki da ma haramta cinikayya a tsakaninsu. Kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afirkar, ECOWAS, ita ce ta yanke wannan shawara a taron kolin da ta yi a kasar Ghana.

Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da jagororin gwamnatin Mali a Bamako suka yi ne dangane da zaben kasar da aka tsara yi cikin watan Fabrairu, zaben kuma da a yanzu suka ce sai bayan shekaru hudu nan gaba.

Shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS, Jean-Claude Brou, ya ce batun jinkirta mayar da Mali bisa mulkin dimukuradiyya ba abu ne da za su lamunta da shi ba.

Taron kolin shugabannin kungiyar raya cigaban kasashen Afirka ta yamma ECOWASHoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

"Hukuma ta fahimci rashin dacewar takardar da Mali ta fitar game da shirin mika mulki a kasar a matsayin wani tsari da ba za mu amince da shi ba. Wannan haramtaccen tsari ne da ya nuna a fili cewa sojoji za su ci gaba da mulkar al’umar Mali na wasu shekaru biyar masu zuwa. Don haka hukuma ta yanke shawarar karfafa takunkumai da aka amince da su tun da fari a kan Mali. Sannan akwai karin wasu takunkumin da suka shafi tattalin arziki wadanda suka dace da matsayar da aka cimma a ranar 12 ga watan Disamba lokacin taron da muka yi a Abuja babban birnin Najeriya."

Wasu matakan sun hada ne da janye dukkanin jakadun kasashen yammacin Afirka da ke Mali da kuma dakatar da harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen da Mali, in banda kayayyakin abinci da magunguna da kayan kula da lafiya musamman wadanda suka shafi yaki da corona da shigar da makamashin mai da wutar lantarki.

Akwai ma batun hana Mali damar amfani da kadarorinta da ke a bankunan kasashen kungiyar ta ECOWAS da duk wani abu da ke da nasaba da samun tallafin kudade.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali Assimi Goita Hoto: Habib Kouyate/XinHua/dpa/picture alliance

Ita ma a nata bangaren kungiyar kasashe masu amfani da kudaden bai daya na CFA wato UEMOA, ta umurci cibiyoyin gudanar da harkokin kudaden kasashen da su dakatar da hulda da Mali ba tare da wani bata lokaci ba, abin da zai sake tsananta wa Mali ta fuskar takunkuman da suka taru a kanta. 

Shugaba Roch Kabore na kasar Burkina Faso, ya ce duk da cewa muna sane da yadda matakan za su takura wa Mali, a tunanimu, samun sauyi a siyasa da batun tattalin arziki da bangaren zamantakewa, za su yiwu ne kawaii dan aka yi zabe ta hanyar da dimukuradiyya ta tsara.

Tuni dai gwamnatin mulkin soja ta Malin, ta yi tir da wadannan matakai na kakaba musu takunkumai da kungiyoyin suka yi.

Sojojin na zargin shugabannin yankin yammacin Afirka, da yi wa manyan kasashen waje aiki.

Ita ma gwamnatin ta soja a Mali ta sanar da janye jakadunta da ke a dukkanin kasashen yammacin Afirka, a matsayin rama abin da kasashen suka yi na janye nasu jakadu daga kasar.